Bayan rashin tabbas da tattalin arziƙin duniya ya fuskanta a shekarar da ta gabata, tattalin arziƙin ya sake gamuwa da cikas sanadiyyar rikicin da ake fama da shi a Gabas ta Tsakiya.
Hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF ta ce ko da rikicin bai yi tsawo ko kuma ya ƙazance fiye da ƙima ba, duk da haka hasashen da aka yi na ci gaban tattalin arzikin duniya a 2026 zai gamu da cikas, inda zai yi rauni zuwa 3.1.
Amma hukumar ta yi gargadin cewa idan yain na Gabas ta Tsakiya ya tsananta, har ya kai ga cewa farashin makamashi ya jijjiga duniya, hasashen ci gaban tattalin arziin duniya zai iya faowa zuwa kashi 2% kacal a shekarar ta 2026.
Haka nan tashin farashin kaya zai iya haura kashi 6% a shekarar 2027.Farashin man fetur da gas ya yi tashin da ba a gani ba a baya-bayan nan tun bayan da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da yaƙi kan Iran.
Iran ta toshe mashigar Hormuz, wata hanyar ruwan teku mai muhimmanci ga sufurin ɗanyen man fetur a duniya, lamarin da ya zama babban abin taƙaddama tsakanin Iran din da Amurka.
Ga jerin ƙasashen da hasashen na hukumar IMF ya ce za su fi samun bunƙasar tattalin arziƙi duk da halin da duniya ke ciki:
Indiya
Indiya ta riƙe matsayinta ta ƙasar da tattalin arziƙinta ke haɓaka fiye da kowace ƙasa a duniya.

