Yaya zan yi a matsayina na sabon ango?

Me ya sa yawancin amare ba su cika yarda da mazansu ba a farkon aure.

A matsayina na wanda yake shirin yin aure, an ce yawancin amare ba su cika yarda da mazansu ba a farkon aure koda suna son junansu, wannan ya sa wadansu suke fada musu da karf, shin hakan ma laifi ne ko kuwa?Amsa: Hakan ai shi ya fi zama laifi saboda ya cutar, saboda tsananin zafin ibadar aure a karon farko ga budurwa, ko tana so ma sai ta sha wahala ina kuma ga ba ta so?

Kuma wata daga wannan fyaden ranar farkon ne sai ta ji ta tsani ibadar aure har ta koma ga Mahaliccinta ba za ta taba kaunatarsa ba balle ta more.

Mafi muhimmancin abin da ya sa hakan ya zama laifi shi ne don ba haka shari’a ta tanada ba.Abin da ya dace a ilimantar da yarinya ilimin ibadar aure tun kafin zuwan daren farko, shi kuma ango ya hada da hakuri ya yi ta rarrashi da dabaru da jan hankali har ya samu hakarsa ta cim-ma ruwa.

Amma yi wa sabuwar amarya ibadar aure da kokawa tana ihu tabbas cin zarafi da rashin sanin mutuncin ta ne.

Tambaya: Anty Nabila ki kara gaya wa maza cewa danne wa mata hakkinsu da yin hulda da su kamar daya daga

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top