INA KUKE IYAYE MATA?
KUZO MU TATTAUNA KAN MATSALAR CIKOWAR NONO LOKACIN SHAYARWA – Breast Engorgement.
👉 Cikowar nono na ɗaya daga cikin matsaloli da ke faruwa ga mai shayarwa, lokacin da nono ya cika sosai da ruwan madara, ya kumbura ya yi tauri da kuma ciwo.
👉 Wannan na iya faruwa musamman a kwanakin farko bayan haihuwa ko idan jariri baya shan nono yadda ya kamata.
MAIKE HADDASA CIKOWAR NONO LOKACIN SHAYARWA.
👉 Rashin shayar da jariri akai-akai.
👉 Jariri baya kama nono yadda ya kamata.
👉 Tsallake lokacin shayarwa.
👉 Taruwar ruwan nono a cikinsa.
👉 Yawan amfani da kwalba ko roba ko fida wajen shayar da jariri.
👉 Daina shayarwa ba zato ba tsammani sakamakon wani dalili.
👉 Yawan cikar nono da madara ba tare da an fitar da ita ba.
👉 Sanya matsatsiyar bra.
👉 Alamomin da mai shayarwa zataji sakamakon cikowar nono sune kamar haka.
1. Nono yana kumbura sosai.
2. Jin alamun nono yana tauri ko É—amewa.
3. RaÉ—adi ko zugin ciwo.
4. Nono yana ɗaukar dumi ko zafi idan an taɓa.
5. Jariri yana wahalar kama nonon saboda taurin sa.
6. Wani lokaci mace na iya samun zazzaɓi kaɗan.
👉 Matakan da za’a É—auka zarar an ji waÉ—annan alamomi sune kamar haka.
1. Ci gaba da shayar da jariri da wannan nonon.
2. Daidaita zaman jariri lokacin shayarwa.
3. A tabbata kan nono ya shiga sosai cikin bakin jariri.
4. A riƙa shayar da jariri akai-akai.
5. A matse ko a furtar da ruwan nono a cikin kofi sannan a shayar da jariri idan ya kasa tsotsa kai tsaye.
6. A matsa ruwan dumi ko sanyi a kan nono zai rage zafi da kumburi.
7. A sanya kaya masu laushi da ba sa matse nono.
8. Nisantar susar kan nono ko matsawa da ƙarfi.
9. Yin tausa hankali da hannu mai tsafta.
10. A garzaya asibiti ko wajen ungozoma idan ba a samu sauƙi ba.
11. Shan magani da ungozoma ko likita suka rubuta.
👉 Rashin ɗaukar mataki da wuri zai iya haifar da matsaloli kamar haka:
1. Ciwon non mai tsanani.
2. Samuwar gyambo ko ƙurji a cikin nono (Breast abscess).
3. Toshewar hanyoyin zuwan nono.
4. Rage yawan ruwan nono.
5. Jariri na iya kasa samun isasshen nono.
6. Jariri zai iya kamuwa da cutar yunwa ko ace jariri ya fara lalacewa.
👉 Domin kaucewa ko rage haɗarin wasu cututtukan da suke faruwa bayan haihuwa sai abi wannan matakan.
1. A fara shayar da jariri cikin awa É—aya bayan haihuwa.
2. Shayar da jariri nono kaÉ—ai a watanni shida na farko idan babu wata matsala.
3. Kada a jira sai nono ya cika sosai kafin shayarwa.
4. Idan akwai ciwo ko kumburi mai tsanani, a tuntuɓi ungozoma ko likita mafi kusa daku.
5. Domin samun ingantaccen bayani da suka shafi lafiyar ku, a cigaba da bibiyar shafin mu da gayyatar abokai da yan uwa.
Www.viralvideo.com.ng
