Wace riba Najeriya ta samu daga cire tallafin man fetur?

Wace riba Najeriya ta samu daga cire tallafin man fetur?🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
Lokaci kamar warhaka a shekaru huɗu da suka gabata, baya ga batun babban zaɓen ƙasar, babbar muhawarar da ta kaure ita ce ta cire tallafin man fetur.

Gwamnatin Najeriya a wancan lokaci ta bayyana wa al’ummarta cewa kuɗin da take kashewa wajen rage tsadar man fetur a ƙasar shi ne dabaibayin da ke hana ta samun ci gaba.

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya bayyana cewa a shakara ta 2022, ƙasar ta kashe kuɗi naira tiriliyan 4.39, wato dala biliyan 9.7 a kan tallafin man fetur.

A wasu shekaru gabanin cire tallafin man fetur ɗin kamfanin na NNPC ya gaza biyan gwamnatin ƙasar kuɗaden harajin da suka kamata daga gare shi, inda ya koka da rashin isassun kuɗi.Najeriya ta dogara ne da man fetur wajen samun kuɗin shiga, kuma gwamnatocin da suka gabata sun yi iyakar bakin ƙoƙarinsu wajen cire tallafin man fetur, amma abin bai yi nasara ba.

Sai a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ranar da aka rantsar da sabon shugaban ƙasar Bola Tinubu, ya sanar cewa daga ranar “tallafin man fetur ya zo ƙarshe”.

Sai dai kimanin shekara huɗu bayan haka al’ummar ƙasa ba su ga wani sauyi ba.

Ƙasar ta ci gaba da cin bashi babu ƙaƙautawa, daga ciki da waje, inda yawan bashin ƙasar ke ci gaba da hauhawa.
Domin samin nishadi
👇👇👇👇👇👇👇👇👇
Www.viralvideo.com.ng

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top