Zargin da ake yi wa shugaban INEC – Ko za su shafi zaɓen Najeriya na 2027?

Yayin da zaɓen Najeriya na 2027 ke ƙara matsowa, haka nan wasu al’umma a ƙasar ke ƙara nuna damuwa game da shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta na ƙasar Joash Amupitan

A cikin ƴan makonnin nan muhawarar da ta kaure a fili da kuma shafukan sada zumunta na ƙasar bisa zargin Amupitan da cewa “ya taɓa nuna goyon baya ga jam’iyyar APC mai mulki”, zargin da hukumar ta musanta.

A makon da ya gabata ƴaƴan jam’iyyar ADC ta ƴan adawar da suka yi haɗaka ta miƙa wa hukumar zaɓen takardar neman Amupitan ya sauka daga muƙaminsa, bisa zargin cewa “ba zai iya gudanar da sahihin zaɓe cikin adalci ba”.

Wannan matsi da sabon shugaban na Inec ke fuskanta abu ne da ba a saba gani a baya-bayan nan, kasancewar akasarin ƴan Najeriya na yi wa shugabannin hukumar da suka shuɗe kallon masu mutunci da kuma tsayawa a tsakiya.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Joash Amupitan a matsayin shugaban hukumar zaɓen Najeriya INEC a watan Oktoban 2025, bayan ƙarewar wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu wanda ya shugabanci hukumar na tsawon shekara 10.
Zargin alaƙa da jam’iyyar APC
Tun a makon da ya gabata ne aka bankaɗo wani shafin X (Twitter) mai ɗauke da sunan shugaban hukumar ta Inec, Joash Ojo Amupitan, da ake zargin nasa ne, inda aka gano cewa ya wallafa wasu ra’ayoyi da suke nuna goyon baya ga jam’iyya mai mulki ta APC a shekarar 2023.

Duk da yake hukumar zaɓen ƙasar ta musanta zargin, inda ta ce Amupitan ba shi da shafi a X, wasu da suka ce sun yi binciken ƙwaƙwaf sun gano lambar waya da kuma adireshin imel masu alaƙa da shafin, wadanda suka ce sun yi daidai da waɗanda shugaban Inec ɗin ya gabatar a lokacin da ya ke aiki a jami’ar jihar Filato da kuma bayanan da ya gabatar kafin naɗa shi muƙamin.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top